Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciƊan takarar shugaban kasar Kenya ya gargaɗi Dangote kan gina matatar mai...

Ɗan takarar shugaban kasar Kenya ya gargaɗi Dangote kan gina matatar mai a kasar

Wani ɗan takarar shugaban ƙasar Kenya, Patrick Osoi, ya gargaɗi hamshaƙin attajirin Najeriya, Aliko Dangote, kan shirin gina matatar mai a Kenya, inda ya ce ba zai amince da gudanar da aikin ba idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasar.

A cikin wani faifan bidiyo da kafar AM Media ta wallafa, Osoi ya bayyana cewa al’ummar Kenya ba sa goyon bayan gina matatar man, don haka ya buƙaci Dangote da ya koma Najeriya domin ci gaba da harkokin kasuwancinsa.

Ya kuma yi barazanar hana aikin idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa, duk da cewa ba a bayar da ƙarin bayani kan dalilan da ya sa yake adawa da gina matatar man ba.

Patrick Osoi na daga cikin ’yan siyasar da ke neman shugabancin Kenya a zaɓen da aka tsara gudanarwa a shekara mai zuwa.

Sai dai har yanzu ba a bayyana martanin Aliko Dangote ko kamfaninsa kan kalaman ɗan takarar ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments