Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNajeriya da Kamaru sun kulla yarjejeniyar ƙarfafa tsaron iyakoki

Najeriya da Kamaru sun kulla yarjejeniyar ƙarfafa tsaron iyakoki

Najeriya da Kamaru sun amince da sabuwar yarjejeniyar haɗin gwiwa domin ƙarfafa tsaro a iyakokinsu, musamman a yankunan kudanci da kuma gaɓar Tekun Guinea.

An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a birnin Yaoundé, bayan tattaunawar kwararru daga ɓangarorin biyu ta ɗauki kwanaki biyu. Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, da takwaransa na Kamaru, Joseph Beti Assomo, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin kasashensu.

Bisa yarjejeniyar, ƙasashen biyu za su ƙara haɗa kai wajen gudanar da sintiri na haɗin gwiwa, musayar bayanan sirri, da kuma horar da jami’an tsaro ta hanyar musayar dakaru. Wannan mataki na daga cikin ƙoƙarin da ake yi na inganta tsaro a kan iyakokin ƙasa da na ruwa.

Haka kuma, za a kafa rundunar sojin ruwa ta haɗin gwiwa domin kula da sintiri a Tekun Guinea, wanda ake ganin zai taimaka wajen kare muradun tattalin arziki da kuma rage ayyukan rashin tsaro a yankin.

Christopher Musa ya kuma bayyana cewa ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da Afirka ke fuskanta shi ne ƙarancin ƙera makamai, don haka Najeriya na neman ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran ƙasashe a fannin bincike da fasahar tsaro.

Kasashen biyu suna da iyakar da ta kai fiye da kilomita 1,900, kuma dukkansu na fuskantar matsalolin tsaro a wurare daban-daban, wanda ya sa wannan haɗin gwiwa ke da matuƙar muhimmanci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments