Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta Najeriya (JAMB) ta sanar da cewa daliban da suka rubuta jarabawar UTME ta shekarar 2026 za su iya fara duba tare da buga asalin takardun sakamakonsu cikin sa’o’i biyu bayan sanarwar da aka fitar.
Sanarwar ta fito ne a ranar Laraba ta bakin mai ba hukumar shawara kan harkokin yaɗa labarai, Fabian Benjamin.
A cewar hukumar, asalin takardar sakamakon UTME ta 2026 na ɗauke da hoton ɗalibi, matsayinsa a jerin sakamakon ƙasa baki ɗaya da kuma wasu matakan tsaro da ake buƙata wajen tantancewa da kuma neman gurbin karatu a manyan makarantu.
Sanarwar ta ce: “Za a fara buga Asalin Takardar Sakamakon UTME ta 2026 cikin sa’o’i biyu daga yau Laraba, 17 ga Yuni, 2026.”
JAMB ta bayyana cewa takardar na daga cikin muhimman takardun da jami’o’i, kwalejoji da sauran manyan makarantu ke buƙata yayin gudanar da tantancewar shiga makaranta (Post-UTME) da kuma bayar da guraben karatu.
Hukumar ta kuma ce ɗalibai za su iya buga takardun sakamakonsu daga kowace na’ura daga gida, wurin aiki ko cibiyoyin kasuwanci da aka amince da su.
JAMB ta shawarci ɗalibai da su tabbatar sun duba dukkan bayanan da ke kan takardar sakamakon kafin su ajiye kwafinta domin amfani da ita a matakan neman gurbin karatu.
An gudanar da babban jarabawar UTME ta 2026 ne a watan Afrilu, yayin da aka sake shirya wata jarabawar cike-gurbi a ranar 13 ga Yuni ga ɗaliban da suka fuskanci matsalolin fasaha ko na tantance bayanan halitta (biometric verification) a lokacin rubuta jarabawar farko.
Hukumar ta fitar da sakamakon jarabawar cike-gurbin a ranar Talata, 16 ga Yuni, 2026.
Tun da farko dai JAMB ta dakatar da fitar da asalin takardun sakamakon domin kammala jarabawar da aka gudanar ga ɗaliban ƙasashen waje da kuma jarabawar cike-gurbin.