Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta sanar da kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen sace wani yaro mai shekara hudu tare da ceto shi cikin koshin lafiya.
Mai magana da yawun rundunar, SP Nafiu Habib, ya bayyana cewa lamarin ya fara ne bayan wani mutum mai shekara 45 ya kai rahoton sace dansa, Musa, wanda aka dauke a gaban gidansu da ke unguwar Gida Dudu Housing Estate a Bauchi.
Binciken farko da ’yan sanda suka gudanar ya nuna cewa wani mutum mai suna Muhammad Usman, mai shekara 39, ya yaudari yaron sannan ya kai shi gidan wani mutum mai suna Hayatudeen Ahmad, mai shekara 40, wanda ke zaune a yankin.
A cewar rundunar, wanda ake zargin ya sanar da abokin nasa cewa yaron dan uwansa ne kuma mahaifiyarsa na fama da rashin lafiya, saboda haka yana bukatar ya zauna da shi na wani lokaci.
Sai dai daga baya bincike ya nuna cewa an rubuta wasikar neman kudin fansa har Naira miliyan biyar daga iyalan yaron.
Bayan samun rahoton, jami’an sashen binciken sirri na rundunar suka fara gudanar da bincike cikin gaggawa, inda suka gano wurin da aka boye yaron tare da kubutar da shi cikin koshin lafiya.
Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin tabbatar da cikakken yadda lamarin ya faru da kuma gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu bayan kammala bincike.