Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroMutuwar Janar Rabe mai ritaya babban abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya...

Mutuwar Janar Rabe mai ritaya babban abin kunya ne ga gwamnatin Najeriya – Masana

Masani a fannin tsaro, Abdullahi Bakoji mai ritaya, ya bayyana cewa kisan tsohon mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, bayan sace shi tare da matarsa, wani babban abin takaici ne da ke nuna yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a Najeriya.

A tattaunawarsa da Iconic Times 24, Bakoji ya ce rasuwar Janar Rabe ta wannan hanya abin takaici ne matuka, musamman idan aka yi la’akari da irin gudunmawar da ya bayar wajen kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Najeriya a lokacin da yake aiki a rundunar soji.

“Abin takaici ne kwarai da kuma abin kunya ga kasa cewa mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare Najeriya ya rasa ransa a hannun masu aikata laifuka bayan an yi garkuwa da shi,” in ji shi.

Ya ce wannan lamari ya kamata ya zama babban abin jan hankali ga gwamnati da hukumomin tsaro domin su sake yin nazari a kan dabarun tsaron da ake amfani da su a kasar nan.

A cewarsa, kisan tsohon janar din ya girgiza zukatan jami’an tsaro masu aiki da kuma wadanda suka yi ritaya, domin yana nuna cewa matsalar tsaro ta kai wani mataki da ke bukatar daukar matakan gaggawa.

Bakoji ya kara da cewa lamarin ya sake bayyana irin gibin da har yanzu dake bangaren tsaro, duk da kokarin da gwamnati da hukumomin tsaro ke yi wajen magance ayyukan ‘yan bindiga da sauran masu aikata laifuka.

Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen yakar matsalar tsaro, tare da samar da sabbin dabaru da hanyoyin da za su taimaka wajen dakile ayyukan masu garkuwa da mutane da sauran masu tada zaune tsaye.

Masanin ya jaddada cewa lokaci ya yi da za a sake duba tsarin tsaro baki daya domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da hana sake afkuwar irin wannan lamari ga sauran ‘yan Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments