Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun hallaka akalla manoma 17 tare da jikkata wasu da dama bayan sun kai hari a kauyen Goron Namaye da ke Karamar Hukumar Maradun a Jihar Zamfara.
Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun isa yankin ne a kan babura, inda da farko suka shiga cikin manoman kamar baki kafin daga bisani su bude musu wuta yayin da suke gudanar da ayyukan noma a gonakinsu.
Rahotanni sun nuna cewa mutane 17 sun rasa rayukansu yayin da wasu 13 suka samu raunuka, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da fargaba.
Mazauna yankin sun ce harin ya faru ne a lokacin da manoma ke kokarin ci gaba da ayyukan noma duk da matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Harin na zuwa ne yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin hare-haren ’yan bindiga a sassan Jihar Zamfara da sauran jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya.