Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroJami’an tsaro sun hallaka ‘yan bindiga 6 a wani artabu a Jihar...

Jami’an tsaro sun hallaka ‘yan bindiga 6 a wani artabu a Jihar Zamfara

Jami’an tsaron hadin gwiwa sun samu nasarar dakile wani hari da ‘yan bindiga suka yi yunkurin kai wa al’ummomin da ke Gundumar Kanoma a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a garin Kanoma da kauyen Gidan Daji, inda jami’an tsaro suka yi artabu da maharan bayan samun bayanan sirri kan motsinsu.

A yayin musayar wutar da aka yi tsakanin bangarorin biyu, an hallaka akalla ‘yan bindiga shida, yayin da sauran suka tsere zuwa cikin dazuka domin tsira da rayukansu.

Majiyoyi sun ce jami’an tsaron sun nuna kwarewa da jajircewa wajen dakile harin, lamarin da ya hana maharan cimma manufarsu ta kai farmaki kan mazauna yankunan.

Bayan artabun, jami’an tsaron sun ci gaba da sintiri da bincike a yankin domin tabbatar da cewa babu sauran barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mazauna yankin sun yabawa kokarin jami’an tsaron, suna masu cewa matakin ya taimaka wajen kare kauyukansu daga hare-haren da suka saba fuskanta daga ‘yan bindiga.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments