Wani ɗalibi mai shekaru 14, mai suna Yahaya Ibrahim Tafida, ɗalibi a Makarantar Sakandaren ‘Yan Sanda ta Minna, ya rasu bayan da tsawar hadari ta same shi a garin Lapai, hedikwatar ƙaramar hukumar Lapai ta jihar Neja.
Wani mazaunin garin, Mohammed Musa, ya shaida wa Daily Trust cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:00 na yamma ranar Litinin, yayin da marigayin da abokansa ke buga ƙwallo a filin wasan Government Girls’ Day Secondary School.
Ya ce lokacin da aka fara ruwan sama tare da iska mai ƙarfi, yaran sun nemi mafaka a ƙarƙashin wata bishiya saboda ba su samu damar komawa gida ba.
Sai dai cikin gaggawa, tsawar walƙiya ta bugi bishiyar, inda Yahaya Ibrahim Tafida ya rasu nan take.
Lamarin ya jefa mazauna yankin cikin jimami da alhini.
Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, bai yi nasara ba, domin ba a samu shigar wayarsa ba kuma bai amsa saƙon da aka tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.