Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiMajalisar Dattawa Najeriya ta amince da kudirin kara yawan alkalan kotun daukaka...

Majalisar Dattawa Najeriya ta amince da kudirin kara yawan alkalan kotun daukaka kara

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da ci gaba da nazarin kudirin dokar da ke neman kara adadin alkalan Kotun Daukaka Kara daga 70 zuwa 110.

Kudirin ya samu amincewar karatu na biyu ne bayan Jagoran Majalisar Dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar da bayanai kan muhimmancinsa a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata.

Masu goyon bayan kudirin sun bayyana cewa karin alkalan zai taimaka wajen rage tarin shari’o’in da ke jiran sauraro tare da inganta saurin yanke hukunci a Kotun Daukaka Kara a fadin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments