Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroAna zargin daya daga cikin dattijan da yan bindiga su ka yi...

Ana zargin daya daga cikin dattijan da yan bindiga su ka yi garkuwa da su ya rasu

Malam Yahaya Billi, daya daga cikin mutanen da aka yi garkuwa da su tare da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Koko/Besse a jihar Kebbi, ya rasu a hannun yan bindiga.

A kwanakin baya ne wani bidiyo ya karade kafafen sada zumunta inda aka ga tsohon shugaban APC da Malam Yahaya Billi suna rokon a taimaka musu daga maboyar ’yan bindiga a dajin Birnin Gwari.

A cikin bidiyon, sun bayyana halin kunci da suke ciki tare da cewa suna fama da rashin lafiya bayan shafe kwanaki suna tafiya a ƙasa.

A lokacin, Malam Yahaya Billi ya kasance cikin mutanen da suka yi kira ga gwamnati da iyalansu da su taimaka wajen ceto su, yana mai nuna damuwa kan tabarbarewar lafiyarsa.

Kungiyar Izalah JIBWIS reshen Ƙaramar Hukumar Koko-Besse ce ta sanar da rasuwarsa, inda ta bayyana cewa za a gudanar da Sallar Jana’izar Ga’ib da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin yau a kofar gidan Sarkin Koko.

Rasuwar tasa na zuwa ne yayin da har yanzu ake jiran samun cikakken bayani kan makomar sauran mutanen da ke hannun masu garkuwa da mutanen.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments