Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaBa mu muke nema Gawuna ba shi ya kawo kansa da bukatar...

Ba mu muke nema Gawuna ba shi ya kawo kansa da bukatar a ba shi takarar gwamna – ADC

Jam’iyyar ADC reshen jihar Kano ta bayyana cewa har yanzu tana ci gaba da tattaunawa da tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar, Nasiru Yusuf Gawuna, dangane da yiwuwar komawarsa jam’iyyar.

Shugaban ADC na jihar Kano, Musa Ungogo, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai.

Ya ce Gawuna ya aike da wasu wakilansa domin fara tattaunawa da shugabannin jam’iyyar kan batun shiga ADC.

A cewarsa, wakilan da suka wakilci Gawuna sun haɗa da tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso, Alhaji Sagir Fanshekara, da Hon. Kadawa. Sun bayyana wa shugabannin ADC cewa Gawuna na da sha’awar komawa jam’iyyar.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa Gawuna ya gabatar da wasu buƙatu kafin yanke shawarar shiga jam’iyyar. Daga cikin buƙatun akwai a tabbatar masa da tikitin takarar gwamna ba tare da fuskantar hamayya ba, tare da bai wa wasu daga cikin magoya bayansa mukamai a cikin tsarin jam’iyyar.

Musa Ungogo ya ce shugabannin ADC sun buƙaci Gawuna da ya gabatar da dukkan buƙatunsa a rubuce domin a yi nazari a kansu tare da duba yiwuwar amincewa da su.

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a cimma wata yarjejeniya ta ƙarshe ba, domin tattaunawar na ci gaba tsakanin ɓangarorin biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments