Masana kimiyyar siyasa irin su Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, ya bayyana cewa rikicin da ya dabaibaye Jam’iyyar NDC ba zai rasa nasaba da sauye-sauyen da ke faruwa a siyasar Najeriya gabanin zaɓen 2027 ba.
A tattaunawar ICONIC TIMES24 da Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa ya ce ɗaya daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalolin cikin gida da ke addabar NDC shi ne yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa domin rage musu ƙarfi a fagen siyasa.
Ya ce ana ƙoƙarin tabbatar da cewa babu wata babbar jam’iyyar adawa da za ta iya yin gogayya mai ƙarfi da jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa, lamarin da ke haifar da rashin daidaito da rikice-rikice a wasu jam’iyyun hamayya.
A cewarsa, wani babban dalili kuma shi ne yadda Jam’iyyar ADC ta fara janye hankalin ‘yan siyasa da dama, inda ta zama tamkar mafakar ‘yan adawa.
Ya bayyana cewa ADC na samun karɓuwa ne saboda yadda ake kallonta a matsayin babbar jam’iyyar hamayya a wannan lokaci, abin da yasa ake ribubun shiga cikinta.
“Mutane da dama suna kallon ADC a matsayin jam’iyyar da za ta iya yin tasiri a zaɓe mai zuwa, har ma wasu na ganin ita ce za ta yi tasiri a nan gaba.
Wannan ne ya sa ake ganin tururuwar masu sauya sheƙa zuwa cikinta,” in ji shi.
A cewarsa, rashin tasirin jam’iyyar a fagen siyasa ya haifar da rashin gamsuwa a tsakanin wasu mambobinta.
Ya ce sakamakon haka ne wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar ke neman hanyoyin ficewa domin samun damar ci gaba da taka rawa a siyasa, inda mafi yawansu ke kallon ADC a matsayin zaɓin da zai ba su damar cimma burinsu na siyasa.