Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanya ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026, domin gudanar da zaɓukan cike gurbi a Kano da wasu jihohi shida.
Shugaban hukumar zabe, Farfesa Joash Amupitan ne ya sanar da hakan a wani biki da aka gudanar a hedikwatar INEC da ke Abuja.
INEC ta yi bayani kan zaben ne yayin maraba da sabuwar kwamishinar zabe Jamila Malafa, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
Rahotanni sun nuna cewa INEC ta ce za a gudanar da zaɓukan cike gurbin tare da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti da aka tsara a rana guda.
A cewar INEC, zaɓukan za su haɗa da kujerun sanatoci a jihohin Enugu, Nasarawa, Rivers da Ondo, da kuma kujera ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi da kujera ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano.
Amupitan ya ce: “Za mu yi wasu zaɓukan da ba su dace da jadawalin yau da kullum ba nan ba da jimawa ba.
An tsara zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a ranar 20 ga Yuni, 2026.
“Za a cike kujerun sanatoci a jihohin Enugu, Nasarawa, Rivers da Ondo, tare da kujera ta Majalisar Dokokin Jihar Kebbi da kuma kujera ta Majalisar Wakilai a Jihar Kano,”