Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaJam'iyyar APC ta kara wa'adin sayar da fom na takarar zaben 2027

Jam’iyyar APC ta kara wa’adin sayar da fom na takarar zaben 2027

APC ta ƙara wa'adin domin masu niyyar neman takara su samu damar mallakar fom

Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ƙara wa’adin sayar da fom na na gani ina so da na tsayawa takara, da kuma miƙa fom ɗin da aka kammala cikewa don zaɓukan 2027.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron shugabanni a ranar Alhamis, mataimakin sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar na ƙasa, Durosinmi Meseko, ya bayyana cewa a yanzu za a rufe sayar da fom ɗin da tsakar daren Litinin, 4 ga Mayu, 2026, yayin da aka tsawaita wa’adin mayar da fom ɗin da sauran takardu zuwa tsakar daren Talata, 5 ga Mayu, 2026.

A baya, an tsara cewa za a fara sayar da fom ɗin daga ranar Asabar, 25 ga Afrilu zuwa Asabar, 2 ga Mayu, 2026, yayin da ranar ƙarshe ta mayar da fom ɗin ita ce Litinin, 4 ga Mayu, 2026.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments