Kotun loli ta Najeriya ta soke taron ƙasa na jam’iyyar PDP da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, a ranakun 15 da 16 ga Nuwamba, 2025.
Alkalan kotu uku cikin biyar sun yanke cewa ƙarar da wani ɓangare na jam’iyyar karkashin jagorancin Tanimu Turaki ya shigar ba ta da tushe.
Babban alkali mai yanke hukunci, Stephen Adah, ya soki jam’iyyar bisa abin da ya kira da cin zarafin tsarin kotu, inda ya ce maimakon su daukaka kara kan umarnin da aka ba su na dakatar da taron, sai suka je wata kotu daban suka sake shigar da ƙara.
Haka kuma kotu ta lura da batun bayar da fom na takarar shugaban jam’iyya ga Sule Lamido.
Sai dai a ra’ayoyin da suka saba, alkalai biyu ciki har da Sadiq Umar sun bayyana cewa kotuna ba su da hurumin shiga cikin wannan batu, domin suna ganin rikicin cikin gida ne na jam’iyya.
Sun kuma ce kotun daukaka kara ta kawo batun rashin bin umarnin kotu da kanta ba tare da bai wa ɓangarorin damar yin bayani a kai ba kamar yadda doka ta tanada.