Hukumomi sun tsaurara matakan tsaro a filin Eagle Square da ke Abuja, inda za a gudanar da babban taron ƙasa na APC na shekarar 2026.
An yi wa dandalin taron ado da launukan jam’iyyar APC – ja, kore, fari, da shuɗi. An ɗaga tutocin jam’iyya suna shawagi a ƙarƙashin rana mai haske da iska mai laushi.
An shirya wuraren zaɓe tare da ginshikan kowane jiha da aka ƙayyade. Ƙungiyoyin tsaro, ciki har da ‘yan sanda, DSS, NSCDC)’, da sauran hukumomin tsaro, suna sintiri da aikin sa ido.
An ga mambobin kwamitin shirya taron, ƙarƙashin jagorancin Dapo Abiodun, suna duba aikin shiri.
Haka kuma an toshe dukkanin hanyoyin da ke kewaye da Eagle Square yayin da jami’an tsaro ke kula da wuraren.
An kuma sauya hanyoyin mota, yayin da wasu mazauna babban birnin tarayya ke tafiya ƙafa zuwa wuraren aikinsu.
Jami’an APC sun ce ana sa ran sama da wakilai 8,000 daga jihohi 36 da Abuja za su halarci taron. Za su samu jagorancin Shugaba Bola Tinubu, gwamnonin jihohi 31, da mambobin majalisar zartaswa.