Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC, Felix Morka, ya bayyana cewa kudain da ake biya domin sayen fom na nuna sha’awa da na tsayawa takara sun tafi ke nan, domin ba a maida wa wanda ya riga biya kudinsa ba.
Morka ya faɗi haka ne ranar Juma’a yayin wata hira a shirin safe na gidan talabijin na Arise TV, inda ya ce ana sa ran masu neman mukami su fahimci sharuddan kafin su biya kudin fom.
Ya ce jam’iyyar na ɗauka cewa duk wanda zai nemi mukami ya san ka’idoji da kuma yankin da mukamin ya shafa kafin ya shiga takara.
A cewarsa, idan mutum ya nemi mukami da ba ya cikin yankinsa, to laifinsa ne, domin ya kamata ya riga ya san inda ya dace ya tsaya takara.
Sai dai ya amince cewa a wasu lokuta na baya, jam’iyyar ta taɓa mayar da kudin ga wasu mutane, amma hakan yana faruwa ne kawai a lokuta na musamman.
Morka ya ƙara da cewa, duk da cewa ba al’ada ba ce a maida kudin, duk wanda abin ya shafa zai iya rubuta takardar neman a dawo masa da kudinsa, sannan jam’iyyar za ta duba bukatar bisa ga yadda ta dace.
Ya ce a takaice, biyan kudin fom yana nufin mutum ya san abin da yake nema, don haka ba a yawan mayar da kudin sai dai idan akwai wani dalili na musamman.