Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro'Yan ta'addan ISWAP sun kashe sojoji 8 a harin Borno

‘Yan ta’addan ISWAP sun kashe sojoji 8 a harin Borno

Maharan sun kai harin a kan babura akalla 70, suka kuma kone sansanin sojojin

Hare-haren da ’yan ta’adda masu alaƙa da ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP) suka kai kan wani sansanin soji a Borno ya yi sanadin mutuwar sojojin Najeriya takwas tare da jikkata wasu 23.

Wasu majiyoyin tsaro uku ne suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Agence France-Presse (AFP) hakan a ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026.

Majiyoyin sun bayyana cewa kimanin mayaƙa 70 na ISWAP ne, ɗauke da babura, suka kai hari sansanin da ke ƙauyen Cross Kauwa, lamarin da ya haddasa mummunan musayar wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

Wani jami’in soja ya ce:

“Sojoji takwas sun biya harajin rayuwarsu, yayin da wasu 23 suka samu raunuka,” yana mai ƙara da cewa harin ya faru ne a ranar Litinin.

Wasu ’yan sa-kai masu yaƙi da ta’addanci da ke taimaka wa rundunar soji sun ce maharan sun taso ne daga sansaninsu da ke tsibirin Dabar Masara a Tafkin Chadi, inda suka yi zagaye mai nisa kafin kai farmakin. Sun kuma tabbatar da adadin waɗanda suka mutu da sauran da suka jikkata.

Wata majiya daga cikin ’yan sa-kan ta ce maharan sun ƙone sansanin gaba ɗaya tare da lalata manyan motocin yaƙi 11, sannan suka kwashe bindigun kariya daga hare-haren sama da aka girka a kan motocin.

Dukkan majiyoyin sun nemi a sakaya sunayensu saboda ba su da izinin yin bayani kan lamarin.

Sansanin da ke da tazarar kilomita 24 daga garin Baga, wanda ya shahara wajen kamun kifi, ya kasance muhimmin garkuwa wajen kare garin daga hare-haren ’yan ta’adda.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments