Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKu yafe min - Tinubu ya nemi gafarar ƴan Najeriya

Ku yafe min – Tinubu ya nemi gafarar ƴan Najeriya

Tunibu ya nemi afuwar yan Najeriya su yafe masa idan ya yi musu wani abun

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ’yan Najeriya su yafe masa idan ya yi musu wani laifi.

Tinubu ya yi wannan roƙon ne yayin buɗe Tafsirin bana a masallacin Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, a jiya Laraba.

Tinubu ya kuma yi magana kan haduwar watan Ramadan da lokacin Azumin mabiya addinin Kirista, yana mai cewa hakan na tunatar da jama’a kan dabi’u da ƙimomin da suke da su na bai daya.

Ya buƙaci ’yan Najeriya na dukkan addinai da su yi addu’a domin samun zaman lafiya tare da mara wa ƙoƙarinsu na yaƙi da ta’addanci, fashi da makami da rashin tsaro baya.

SourceIconic FM
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments