Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaIna cikin kwanciyar hankali a PDP – Seyi Makinde

Ina cikin kwanciyar hankali a PDP – Seyi Makinde

Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ziyarci shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ya ce ya kai ziyarar ne domin tattaunawa da shugaban kasa kan “wasu batutuwan da suka shafi mulki” ba na siyasa ba.

Ganawar dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ci gaba da samun sauye-sauye a siyasa, gabanin babban zaɓen ƙasar na 2027.

A baya, wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka haɗa da gwamnoni sun fice daga jam’iyyar zuwa APC, inda suka bar Makinde da wasu tsiraru a jam’iyyar ta adawa.

Da aka tambaye shi ko zai koma APC nan ba da jimawa ba, Makinde ya jadada cewa hankalinsa a kwance ya ke a PDP.

Ya ce:

”Hankali na a kwance ya ke a PDP. Waɗansu abubuwa na iya tasowa a ƙasar nan da ake buƙatar a yi watsi da batun ɓangaranci, inda ba zai zama batun wataƙila APC ta yi magana ita kaɗai ko PDP ta yi magana ita kaɗai ba.”

Ya yi nuni da cewa, yayin da shi da Shugaban ƙasar ke jam’iyyun siyasa daban-daban, ci gaban Najeriya ya kasance wani aiki ne da ya kamata duka ƴan kasa su damu da shi ba tare da la’akari da ra’ayin siyasa ba.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments