A jiya Alhamis, 22 ga watan Janairu, 2026 Amurka ta sanar da kawo karshen tallafin da ta ke bayar wa a hukumar Lafiya ta Duniya WHO, duk kuwa da kasancewarta jigo wajen samar da kuɗaɗen tafiyar da hukumar da ke samar da tallafin magunguna da sauran ɓangarorin lafiya ga ƙasashe da dama musamman masu tasowa.
Rahotanni daga ƙasashen duniya sun bayyana cewa ana zargin hukumar da kasancewa ƙarƙashin tasirin China, ana alakanta hukumar da cewa ta kasa shawo kan wasu matsaloli a lokacin bulluwar cutar Covid- 19.
Jim kaɗan bayan shigarsa pfishi a bara, Donald Trump ya sanar da aniyar janyewar ƙasarsa daga hukumar, kodayake tun a wancan lokaci ya ƙulla yarjejeniyar cewa sai bayan shekara guda ne ficewar za ta fara aiki a hukumance wato ranar 22 ga watan Janairun 2026.