Dakarun rundunar haɗin gwuiwa ta Arewa maso Gabas (JTF) ƙarƙashin Operation Haɗin Kai, a cikin shirin Operation ‘Desert Sanity V,’ sun yi nasarar daƙile wani shirin ƙwanton ɓauna da ƴan Boko Haram suka tsara a yankin Sambisa da Mandara Mountains a ranar Alhamis, 22 ga Janairu, 2026.
A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na OPHK, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar a safiyar Juma’a a Maiduguri, ya ce ƴan ta’addan sun yi yunƙurin kai hari ta amfani da bama-baman da aka binne a gefen hanya da kuma ruwan wuta mai ƙarfi.
Sai dai dakarun sashi na 1 sun mayar da martani a cikin ƙwarewe, inda suka kashe ƴan ta’adda 10, ciki har da manyan kwamandoji biyu da aka bayyana sunayensu da Basulhu da Ubaida.
Sanarwar ta ce bin sawunsu da aka yi bayan artabun ya haifar da ƙwato makamai da kayan aiki da dama, ciki har da bindigu AK-47 guda uku, da bindigar ‘pump-action’ guda ɗaya, da babura biyar, da gurneti guda biyu, da rediyon Baofeng guda biyu, da sinƙin harsashi 12 na AK-47, da na’urar harba roka (RPG charger), da igiyoyinE tayar da bam, da batura, da bandoliya, da jakunkunan ruwa da kuma kayan haɗa bama-bamai.