Saturday, October 17, 2026
HomeTsaro‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 32 tare da kashe...

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane 32 tare da kashe mutum daya

Wasu Yan bindiga sun sace mutane 32 da kuma kashe wani mutum 1

Ana fargabar cewa ‘yan bindiga sun sace mutane 32, ciki har da mata da ƙananan yara, a wani hari da suka kai garin Kadagen Kauru da ke ƙaramar hukumar Kauru a Jihar Kaduna.

Sun kuma kashe mutum ɗaya a yayin kai harin. Wani mazaunin garin ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 12:30 na dare.

Ya bayyana cewa daga cikin waɗanda aka sace akwai mata masu juna biyu da jarirai, kuma an jikkata mutane biyu amma sun warke.

Harin ya auku ne bayan wani makamancin irinsa da aka kai maƙwabtan ƙauyuka a baya-bayan nan, inda aka sace mutane da dama.

Mazauna yankin sun ce suna rayuwa cikin fargaba saboda yawaitar hare-haren ‘yan bindiga.

Shugaban ƙaramar hukumar Kauru ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana ɗaukar matakai. Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta ce za ta binciki lamarin.

Jihar Kaduna dai ta daɗe tana fama da matsalar tsaro, musamman a yankunan karkara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments