Ana sa ran Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zai gana da tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje a yau.
An ce taron zai haɗa manyan shugabannin APC a Kano, ciki har da Sanata Barau Jibrin, domin kammala shirin sauya sheƙar gwamnan.
Hakan dai na zuwa ne gabanin yunkurin sauya sheƙarsa daga NNPP zuwa jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya wanda ya rikita siyasar jihar Kano.
Bayanan dai sun fito ne daga Muhammad Garba, babban sakataren Ganduje yayin wata tattaunawa a gidan rediyo.
Garba ya ce taron zai share fagen sauya sheƙar gwamnan a Kano, inda manyan shugabannin APC za su halarta domin cimma matsaya ta ƙarshe game da barin gwamnan NNPP.
Ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin da shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, za su halarci taron.
Muhammad Garba ya ce zuwan Abba Kabir zai ƙara ƙarfin APC wajen tunkarar zaɓe a faɗin ƙasar nan, ta hanyar gina kyakkywar alaka da samun bayanan mambobi.