Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaSai na san matsayin da zan samu kafin na koma APC -...

Sai na san matsayin da zan samu kafin na koma APC – Kwankwaso

Kwankwaso ya jaddada cewa dole ne sai ya San matsayin sa kafin ya koma jam’iyyar APC

Jagoran jam’iyyar NNPP kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce ba zai koma jam’iyyar APC ba sai an fayyace masa matsayinsa a jam’iyyar kuma sai an dawo da takardun manufofin da suka rubuta kan yadda za a tafiyar da rayuwar talakawan Najeriya.

Kwankwaso ya jaddada cewa dole ne a fayyace masa matsayin magoya bayansa da kuma gwamnatin jihar Kano kafin ya yanke duk wata shawara.

Kwankwaso dai ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a gidansa da ke Miller Road a Kano, yayin da yake karɓar shugabanni da magoya baya daga ƙananan hukumomin Rano da Dawakin Tofa, tare da wasu mambobin tafiyar Kwankwasiyya da suka sake jaddada biyayyarsu ga jam’iyyar NNPP.

Jagoran ya bayyana cewa “Idan har zan koma jam’iyyar APC dole ne a sanar da ni matsayi na a cikin jam’iyyar, sai an faɗa mana abubuwan da za a yi mana sannan kuma sai mun san matsayin jihar Kano da magoya bayanmu.”

Kwankwaso ya bayyana cewa burinsa shi ne kare muradun al’umma, musamman talakawa, tare da tabbatar da cewa duk wata tafiya ta siyasa za ta amfanar da magoya baya da kuma jama’ar jihar Kano gaba ɗaya.

Wannan furuci na Kwankwaso na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta raɗe-raɗin yiwuwar sauya sheƙar gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC.

SourceBBC
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments