Sunday, October 18, 2026
HomeIlimiGwamnatin tarayya ta fito da sabbin matakan hana satar jarrabawa

Gwamnatin tarayya ta fito da sabbin matakan hana satar jarrabawa

Matakan za su fara aiki daga 2026 domin inganta jarabawar WAEC da NECO a fadin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta bayyana sabbin dabaru da za ta fara aiwatarwa daga shekarar 2026 domin dakile satar jarabawa a jarabawar Hukumar Jarabawar Afrika ta Yamma (WAEC) da Hukumar Jarabawar Kasa (NECO), a wani yunkuri na inganta sahihanci da tsarin tantance ilimi a Najeriya.

Ministan Ilimi, Dakta Morufu-Tunji Alausa, tare da Karamin Ministan Ilimi, Farfesa Suwaiba Ahmed, ne suka sanar da hakan a Abuja a ranar Litinin.

Sun bayyana cewa sauye-sauyen sun mayar da hankali ne kan kara gaskiya da tsaurara kulawa a dukkan matakan gudanar da jarabawar kasa.

Wannan bayani ya fito ne cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, Boriowo Folasade, ya sanya wa hannu.

Sanarwar ta ce ma’aikatar ta kuduri aniyar magance matsalolin satar jarabawa da wasu kura-kuran da suka dade suna damun jarabawar jama’a.Daga cikin manyan matakan da aka jero akwai amfani da fasaha ta zamani da tsauraran dokokin gudanarwa domin kare mutuncin jarabawar WAEC da NECO.

Haka kuma, za a fara tsarin gauraya da jeranta tambayoyi ta hanyoyi daban-daban.

Duk da cewa É—alibai za su amsa tambayoyi iri daya, tsarin da jerin tambayoyin zai bambanta daga É—alibi zuwa É—alibi, lamarin da zai rage yiwuwar hadin baki a dakin jarabawa.

Gwamnatin ta kuma sake jaddada matsayinta kan sauya makaranta a matakin aji uku na sakandare (SS3), tana mai gargadin cewa za a fara aiwatar da dokar da ke hana irin wannan sauyi ba tare da sassauci ba.

Ma’aikatar ta tunatar da cewa an riga an haramta sauya makaranta a wannan mataki ta wata sanarwa ta hukuma, domin dakile sauye-sauyen gaggawa da ke da alaka da satar jarabawa.

Haka zalika, an amince da sabbin ka’idojin kasa kan tasa-tasai, inda dukkanin hukumomin jarabawa za su bi tsayayyun lokutan mika bayanai.

An tanadi lokutan mika bayanan zangon karatu na farko a Janairu, na biyu a Afrilu, sannan na uku a Agusta, domin tabbatar da daidaito da sahihancin bayanai.Domin kara sa ido, gwamnati za ta kaddamar da lambar shaidar ɗalibi ta musamman (Examination Learners’ Identity Number) ga kowane dalibi.

A cewar ma’aikatar, wannan lamba za ta taimaka wajen bin diddigin dalibai, da tallafa wa dogon shirin gyaran tsarin tantancewa da bayar da shaidar kammala karatu.

Ministocin sun tabbatar wa masu ruwa da tsaki cewa za a gudanar da jarabawa karkashin kulawa mai tsauri tare da hadin gwiwar hukumomin jarabawa, domin tabbatar da bin ka’idojin da’a.

Sun jaddada cewa matakan na nuna kudurin Gwamnatin Tarayya na gudanar da jarabawa da gaskiya, adalci, kuma daidai da ka’idojin duniya, bayan la’akari da halin da ilimi ke ciki a Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments