Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroƳan bijilanti sun cafke miyagun ƙwayoyi a Taraba, an kama mutum ɗaya

Ƴan bijilanti sun cafke miyagun ƙwayoyi a Taraba, an kama mutum ɗaya

Ƴan bijilanti a Jalingo sun dakile safarar manyan miyagun ƙwayoyi da ake zargin hodar iblis ne

Rundunar bijilanti a Jihar Taraba, ta kama miyagun ƙwayoyi da ake zargin hodar iblis ce a babban birnin jihar, Jalingo.

Rundunar ta ce an kama kayan biyo bayan sahihan bayanai da suka samu game da safarar miyagun ƙwayoyi a cikin jihar a karshen mako.

“Bisa ga wannan bayanin, jami’anmu sun kaddamar da aikin leken asiri wanda ya kai ga dakile raba kwayoyin kafin a rarraba su,” in ji Kwamandan Rundunar Taraba, Bello Arabi.

Arabi ya bayyana cewa an tsare mutum ɗaya da ake zargi a alaqa da wannan batu, sannan an mika shi da kayan da aka samu ga Hukumar Kula da Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) don ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da shi a gaban kotu.

Ya yaba da jajircewa da ƙarfin guiwar jami’an da suka gudanar da aikin, yana mai cewa wannan kama kayan ƙwayoyi babban ci gaba ne wajen yaki da rashin tsaro a jihar.

Kwamandan ya ce shan miyagun ƙwayoyi na jawo aikata laifuffuka.a yi kira ga dukkanin jami’an bijilanti a jihar da su kasance cikin shiri, su ƙara ƙoƙarin yaki da laifuffukan da suka shafi ƙwayoyi.

Arabi ya kuma tabbatar da ci gaba da haɗin gwiwa tsakaninsu da hukumomin tsaro na ƙasa, musamman NDLEA, domin tabbatar da tsaro ga mazauna jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments