Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaKwamitin zartarwar NNPP ya nada Zubair Abiya a matsayin Shugaban rikon jam’iyyar

Kwamitin zartarwar NNPP ya nada Zubair Abiya a matsayin Shugaban rikon jam’iyyar

Kwamitin zartarwar NNPP ya nada Zubair Abiya a matsayin Shugaban rikon jam’iyyar ta Kano bayan sauke Hashim Dunguraws

Kwamitin zartarwa na jam’iyyar NNPP a Jihar Kano ya amince da naɗin Hon.

Abdullahi Zubairu Abiya a matsayin shugaban jam’iyyar na riko, biyo bayan korar tsohon shugaban jam’iyyar na jiha, Malam Hashimu Dungurawa.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan na cikin sanarwar da mataimakin mai ba jam’iyyar shawara kan harkokin shari’a, Barrista Yusuf Mukhtar, ya fitar bayan taron gaggawa da kwamitin zartarwa na jam’iyyar ya gudanar a Kano.

Sanarwar ta ce naɗin Abiya ya biyo bayan gabatar da rahoto da ƙudurin korar da aka mika daga kwamitin zartarwa na Karamar Hukumar Dawakin Tofa, wanda ya samo asali daga matakin da kwamitin zartarwa na mazaɓar Gargari ya ɗauka kan Dungurawa bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa dokokin jam’iyyar.

Rahoton ya nuna cewa kwamitin zartarwa na Gargari ya amince da ƙudurin korar Dungurawa ne a taronsu na biyu da suka gudanar makonni biyu bayan babban zaɓe, kafin a tura shi zuwa matakin karamar hukuma sannan daga bisani zuwa matakin jiha.

Bayan nazarin rahoton, kwamitin zartarwa na NNPP a matakin jiha ya amince da ƙudurin tare da tabbatar da Abiya a matsayin shugaban jam’iyyar na riko a Kano.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments