Ƙyaftin ɗin tawagar Portugal, Cristiano Ronaldo ya ce ba zai yi ritaya daga buga tamuala ba, har sai ya zura ƙwallo 1,000 a raga.
Ronaldo mai shekara 40 ya ci wa Al-Nassr ƙwallo biyu a wasan da suka doke Al Akhdoud 3-0 a gasar tamaula ta Saudiyya ranar Asabar, kenan jimilla ya zazzaga 956 a raga a wasan da ya buga wa ƙungiyoyi da kuma Portugal.
Wanda ya koma taka leda a Al-Nassr a 2022, Ronaldo ya saka hannu a kan yarjejeniyar a watan Yuli.
Zai ci gaba da wasa a ƙungiyar da ke buga gasar tamaula ta Saudiyya har zuwa lokacin da zai haura shekara 42 da haihuwa.
A wani jawabi da ya yi lokacin da aka bayyana shi a fitatcen ɗan ƙwallon Gabas ta tsakiya na bana a ranar Asabar, Ronaldo ya ce:
“Buri na a kwallon kafa yana da yawa kuma ina so in ci gaba da taka leda. Zan iya buga wasa, ko a Gabas ta Tsakiya ko a Turai.”
“Kullum ina jin daɗin buga ƙwallon kafa kuma ina so in ci gaba da bugawa.”
“Kun san burina. Ina so in lashe kofuna, kuma ina so in ci ƙwallo 1,000 kamar yadda dukkanku kuka sani. Tabbas zan kai wannan adadi, muddin ban samu rauni ba.”
A wata hira da ya yi da Piers Morgan a watan da ya gabata, Ronaldo ya ce yana shirin yin ritaya daga buga kwallon kafa “ba da jimawa ba”.
“Na yi tunanin zan fara shirye-shiryen ritaya. Abu ne mai wahala, tabbas. Wataƙila zan yi kuka a lokacin,” in ji Ronaldo.