Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa ga Abdulmalik Tanko, wanda aka samu da laifin garkuwa da kuma kashe Hanifa, yarinya ’yar shekara takwas.
Rahotanni sun bayyana cewa, Mai shari’a A.R. Muhammad ne ya bayyana hakan yayin yanke hukuncin kotun, inda ya tabbatar da hukuncin da kotun ƙasa ta yanke a baya kan laifukan da aka tuhumi Abdulmalik Tanko.
A yayin hukuncin, mai shari’a A.R. Muhammad ya ja hankalin gwamnati kan muhimmancin gaggauta aiwatar da hukuncin kisa da kotu ta yanke, domin tabbatar da aiwatar da adalci da kuma kare al’umma.