Gwamnatocin ƙasashen Tarayyar Turai sun amince su ci gaba da riƙe ko dakatar da kadarorin Rasha na sama da Dala miliyan dubu biyu, da suka dakatar da gudanarsu a yankin ƙasashen na -EU, tun bayan da Rasha ta mamayi Ukraine.
An riƙe yawancin kuɗin gwamnatin Rasha ne a bankin Euroclear na Belgium.
Shugabannin Turai na sa ran cimma wata yarjejeniya a mako mai zuwa wadda a ƙarƙashinta za a yi amfani da kuɗin a bayar da bashin taimaka wa gwamnatin Ukraine.
Ukraine dai na fuskantar matsalar rashin kuɗi ne bayan an shafe shekara huɗu ana yaƙi, a don haka ƙasashen Turai ke son taimaka mata saboda kawancen da ke tsakaninsu.
A kan wannan kudiri jami’an Rasha sun zargi kungiyar ta Turai da sata.
A ranar juma’ar da ta gabata ne babban bankin Rasha ya ce zai shigar da bankin na Belgium -Euroclear ƙara a wata kotu a Moscow saboda shirin bayar da bashin kuɗin.