Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeƘasashen Turai na shirin ba wa Ukraine bashi daga cikin kuɗaɗen Rasha...

Ƙasashen Turai na shirin ba wa Ukraine bashi daga cikin kuɗaɗen Rasha da aka daskarar

Gwamnatocin ƙasashen Tarayyar Turai sun amince su ci gaba da riƙe ko dakatar da kadarorin Rasha na sama da Dala miliyan dubu biyu, da suka dakatar da gudanarsu a yankin ƙasashen na -EU, tun bayan da Rasha ta mamayi Ukraine.

An riƙe yawancin kuɗin gwamnatin Rasha ne a bankin Euroclear na Belgium.

Shugabannin Turai na sa ran cimma wata yarjejeniya a mako mai zuwa wadda a ƙarƙashinta za a yi amfani da kuɗin a bayar da bashin taimaka wa gwamnatin Ukraine.

Ukraine dai na fuskantar matsalar rashin kuɗi ne bayan an shafe shekara huɗu ana yaƙi, a don haka ƙasashen Turai ke son taimaka mata saboda kawancen da ke tsakaninsu.
A kan wannan kudiri jami’an Rasha sun zargi kungiyar ta Turai da sata.

A ranar juma’ar da ta gabata ne babban bankin Rasha ya ce zai shigar da bankin na Belgium -Euroclear ƙara a wata kotu a Moscow saboda shirin bayar da bashin kuɗin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments