Kasar Cambodia ta bayyana cewa Thailand na ci gaba da jefa bama-bamai a cikin yankinta, ƴan sa’o’i kaɗan bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa ƙasashen biyu sun amince da dakatar da rikici a kan iyakokinsu.
Sabon rikicin tsakanin ƙasashen biyu na kudu maso gabashin Asiya ya samo asali ne daga tsohon rikicin iyaka da aka gada tun zamanin mulkin mallaka, wanda ya shafi kusan kilomita 800 na iyaka, rikicin da ya tilasta wa kimanin mutane rabin miliyan tserewa daga gidajensu a ɓangarorin biyu.
Kowanne ɓangare dai na zargin ɗayan da sake tayar da rikicin, yayin da ake ci gaba da musayar wuta a wasu sassan iyakar duk da iƙirarin cewa an cimma matsaya kan tsagaita wuta.
Hakan dai na zuwa ne bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Thailand da Cambodia sun amince da dakatar da faɗa a kan iyakar da ake taƙaddama a kai, rikicin da rahotanni suka ce ya kashe aƙalla mutane 20 a cikin makon nan.
A baya-bayan nan dai Amurka, China da Malaysia a matsayinta na shugabar ƙungiyar ASEAN ta ƙasashen yankin Asiya sun shiga tsakani, inda suka taimaka wajen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Yuli.