Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaAPC ta yi wa gwamnan Ribas rajista a hukumance

APC ta yi wa gwamnan Ribas rajista a hukumance

Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya samu rijistar zama ɗan jam’iyyar APC bayan ya karɓi katin zama ɗan jam’iyyar a gidan gwamnati da ke Fatakwal

.

Shugaban jam’iyyar APC reshen jihar Ribas, Tony Okocha, wanda ya wakilci shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya miƙa katin ga Fubara a jiya juma’a.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Fubara ya ce ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne da nufin bunƙasa haɗin kai da ci gaban jihar Ribas.

Fubara ya ce samun daidaito da jam’iyya mai mulki a matakin tarayya ya zama wajibi don tabbatar da zaman lafiyar siyasa da kuma ci gaba a faɗin jihar.

Gwamnan ya jaddada cewa a yanzu da jihar Ribas ta haɗe a ƙarƙashin inuwa ɗaya da gwamnatin tarayya, aikin da ke gabansa na ƙarfafa jam’iyyar APC.

Bikin ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo (SAN).

SourceBBC hausa
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments