Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiGwamnatin Kano ta fara shirin daukar malamai 4,000 a jihar

Gwamnatin Kano ta fara shirin daukar malamai 4,000 a jihar

Gwamnatin Abba na shirin kara yawan malamai domin inganta ilimi tun daga matakin farko

Hukumar ilimin bai daya ta Kano (SUBEB) ta sanar da shirin daukar karin malamai 4,000 domin inganta koyar da Lissafi da Turanci a makarantun firamare da na sakandaren farko a fadin jihar.

Shugaban hukumar, Yusuf Kabir, ya bayyana wannan shiri a yayin taron duba sakamakon bincike koyo na 2025 da aka gudanar a Kano, tare da goyon bayan shirin PLANE na gwamnatin Birtaniya.

Ya ce duk da cewa jihar ta dauki malamai 4,343 a baya-bayan nan, akwai kananan hukumomi da dama da har yanzu ke fama da karancin malamai.

Za a gwada malamai kafin daukar su aiki

Kabir, wanda Sakatariyar SUBEB, Hajiya Amina Umar, ta wakilta, ya ce hukumar na kammala shirye-shirye a cibiyoyi bakwai na jarabawar kwamfuta da ke Wudil, Bichi da wasu wurare, inda za a gudanar da gwajin cancantar masu nema.

Ya bayyana cewa a wasu makarantu, malami guda yana kula da dalibai har 132, al’amarin da yake rage ingancin koyarwa.

A cewarsa, hukumar na kokarin rage cunkoson aji ta hanyar tabbatar da tsarin malami daya ga dalibai 60, domin inganta ilimin yara a duk fadin jihar.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments