Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan Kwadago, Chris Ngige, a gaban Mai Shari’a Mariam Hassan na Babbar Kotun birnin tarayya da ke Gwarinpa.
Ana tuhumar sa da laifuffuka takwas, sannan ya iso kotun tare da jami’an EFCC misalin ƙarfe 8:10 na safe. A cikin shari’ar da aka yi wa lamba FCT/HC/CR/726/2025.
A cikin takardar tuhumar mai ɗauke da kwanan wata 31 ga Oktoba, kuma aka shigar da ita 9 ga Disamba, lauya mai jagoranci Sylvanus Tahir (SAN) ya zargi Ngige da aikata laifuka ne yayin da yake Ministan Kwadago a zamanin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Zarge-zargen da EFCC ke yi wa Ngige
A zargin farko, EFCC ta zargi Ngige da amfani da mukaminsa tsakanin 2015 zuwa 2023 wajen bai wa kamfanin Cezimo Nigeria Limited fifiko ba bisa ka’ida.
Kamfanin na hannun abokinsa, Ezebinwa Amarachukwu Charles, inda aka ce an ba shi kwangila guda bakwai na horaswa, bayar da kayan aiki da sauran ayyuka, jimillar ₦366,470,920.68.
A zargi na biyu, EFCC ta ce Ngige ya ba wa kamfanin Zitacom Nigeria Limited, wanda shi ma na abokinsa ne, kwangila guda takwas da kudinsu ya kai ₦583,682,686.
A tuhuma ta uku kuma, ana zargin Ngige da ba wa Jeff & Xris Limited, mallakin Nwosu Jideofor Chukwunwike, kwangila takwas na ayyuka daban-daban da suka kai ₦362,043,163.16.
A tuhuma ta huɗu, an zargi Ngige da amfani da mukami wajen ba wa Olde English Consolidated Limited, kamfanin da ke da alaƙa da Uzoma Igbonwa, kwangila hudu da kudinsu ya kai ₦668,138,141.
A tuhuma ta biyar, an kuma zarge shi da bayar da wasu kwangila hudu ga Shale Atlantic Intercontinental Services Limited, mallakin Uzoma Igbonwa, da jimillar su ₦161,604,625.
Dukkannin waɗannan zarge-zargen sun sabawa Sashe na 19 na Dokar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa, 2000.
Ana zargin Ngige da karbar ‘kyaututtuka’ daga kamfanoni
A tuhuma ta shida, an zargi Ngige da karɓar ₦38,650,000 ta hanyar kungiyar sa ta Chris Nwabueze Ngige Campaign Organisation daga kamfanin Cezimo Nigeria Limited, yayin da yake Ministan Kwadago.
A tuhuma ta bakwai, an ce ya karɓi ₦55,003,000 ta hanyar Chris Ngige Scholarship Scheme daga Zitacom Nigeria Limited, duk kuwa yana a kan aiki a matsayin minista.
A tuhuma ta takwas, an kuma zarge shi da karɓar ₦26,130,000 daga Jeff & Xris Limited ta hanyar kungiyar tallafin karatu ta Chris Ngige Scholarship Scheme.
EFCC ta ce waɗannan laifuffuka sun sabawa Sashe na 17(a) na Dokar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta 2000, kuma hukuncinsu yana ƙarƙashin Sashe na 179(c) na irin wannan doka.