A wani yunkuri na sake fasalin ilimi ta hanyar fasahar zamani a Najeriya, Afrika da sauran sassan duniya, Iconic Open University ta sake kaddamar da sabuwar cibiyar karatu ta ‘The Harmony Campus,’ a birnin Ilorin, babban birnin Jihar Kwara.
Wannan matakin ya zama muhimmin ci gaba a tarihin faɗaɗa ayyukan babbar jami’ar mai zaman kanta a Najeriya, inda take ƙara miƙa tsarin ilimi mai sassauci da dogaro da fasaha, tare da tallafin karatu na zahiri ga ɗalibai a Jihar Kwara da kewaye.
Cibiyar Harmony ba wai gini kawai ba ce; An tsara ta ne domin karya shingayen gargajiya a fannin ilimi ta hanyar haɗa karatun nesa da na yanar gizo da kuma tallafin ilimi a wurin karatu.
Ta wannan cibiya, ɗalibai za su iya samun ingantattun kayan karatu, yin mu’amala da takwarorin su, da kuma samun jagoranci da shawarwari kai tsaye daga malamai, yayin da suke ci gaba da more sassaucin tsarin karatu da Jami’ar Iconic Open University ta shahara da shi.
Cibiyar na kan titin Ibrahim Taiwo, a tsakiyar birnin Ilorin, lamarin da ke sauƙaƙa samun ilimin jami’a ga dubban masu neman ilimi da ɗaliban da ke karatu a yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.
Haka zalika ‘The Harmony Campus’ na nuna kyakkyawan tarihin Jihar Kwara na zaman lafiya, haɗin kai da zaman tare na al’adu daban-daban.
Jami’ar dai na ci gaba da faɗaɗa ayyukanta a faɗin Najeriya da ma ƙasashen waje.