Monday, October 19, 2026
HomeLabaraiShugaba Tinubu na shirin gabatar da daftarin kasafin kudin 2026 ga Majalisun...

Shugaba Tinubu na shirin gabatar da daftarin kasafin kudin 2026 ga Majalisun Tarayya.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, zai gabatar da daftarin kasafin shekarar 2026.

Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun sanar da shirin karɓar daftarin kasafin kuɗin shekarar 2026 a hukumance, yayin zaman haɗin gwuiwa da aka shirya gudanarwa a ranar Juma’a.

Sanarwar na ƙunshe ne a wata wasiƙa da Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya karanta a zauren majalisar a ranar Alhamis, inda shi ma Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta makamanciyar wasiƙa a zauren Majalisar Dattawa.

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, zai gabatar da daftarin kasafin shekarar 2026 da misalin ƙarfe 2 na ranar Juma’a, tare da sa ran zaman zai koma zauren Majalisar Wakilai da misalin ƙarfe 1:45 na rana.

A wani ɓangare kuma, Majalisar Dattawa ta karɓi wasiƙu biyu daban-daban daga Shugaban Ƙasa Tinubu, inda yake neman tabbatar da naɗin shugabannin hukumomin kula da harkokin man fetur, bisa tanade-tanaden dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 (PIA).

A wasiƙar farko, Shugaban Ƙasa ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin Injiniya Saidu Muhammad, a matsayin Babban Shugaban Hukumar Kula da Man Fetur ta ƙasa (NMDPRA), bisa sashe na 41(6) na PIA 2021, yana mai bayyana cewa wannan naɗi ya biyo bayan murabus ɗin tsohon Babban Shugaban hukumar.

A wasiƙa ta biyu kuma, Shugaban Ƙasa ya nemi tabbatar da naɗin Mista Oritsemanori Sewa Inyosa, a matsayin Babban Shugaban Hukumar Kula da bayar da lasisin dakon man fetur zuwa ƙasar nan (NUPRC), bisa sashe na 11(3) na Dokar PIA 2021, inda dukkan naɗe-naɗen aka miƙa su ga Kwamitin Majalisa domin gaggauta duba su tare da yiwuwar amincewa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments