Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ’yan takarar gwamnan Jihar Kano guda 17, amma sunan ɗan takarar jam’iyyar NDC, Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo, bai bayyana a cikin jerin ba.
An fitar da jerin sunayen ne a ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2026, inda aka lura cewa sunan tsohon mataimakin gwamnan Kano bai bayyana cikin sunayen ’yan takarar da hukumar ta wallafa ba.
Sai dai, INEC ba ta bayyana dalilin da ya sa sunan Gwarzo bai bayyana a cikin jerin ba, kuma babu ƙarin bayani daga hukumar kan matakin da ta ɗauka game da takararsa.
Aminu Abdussalam Gwarzo dai an zaɓe shi a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC a watan Mayun 2026, gabanin zaɓen gwamnan jihar na shekarar 2027.
Har yanzu, ba a bayyana ko rashin sunan nasa a jerin da aka fitar yana da alaƙa da wata matsala ta takara ko kuma wani dalili na daban ba.