Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaZan zama shugaban ƙasa bayan zaben 2027 – Sowore

Zan zama shugaban ƙasa bayan zaben 2027 – Sowore

Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, ya bayyana kwarin gwiwar cewa zai lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa zai zama shugaban Najeriya bayan zaɓen.

Sowore ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan matakin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya DSS na neman dakatar da shari’ar da take yi masa har zuwa bayan zaɓen 2027.

A baya, DSS ta umarci lauyanta, Akinlolu Kehinde, SAN, da ya nemi Babbar Kotun Tarayya ta dakatar da sauraron ƙarar da ake yi wa Sowore domin bai masa damar gudanar da yakin neman zaɓensa da sauran ayyukan siyasa ba tare da shari’ar ta zama masa cikas ba.

A wani saƙo da Sowore ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Lahadi, 30 ga Agusta, 2026, ya ce a ganinsa ba za a sake ci gaba da shari’ar ba bayan zaɓen, domin yana hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Darakta-Janar na DSS, Tosin Ajayi, ba za su ci gaba da riƙe mukamansu ba.

Sowore ya zargi gwamnatin da amfani da hukumomin gwamnati wajen matsa wa abokan hamayyar siyasa lamba, yana mai cewa idan ya samu nasara, zai kawo ƙarshen abin da ya kira tsangwamar siyasa da amfani da hukumomin gwamnati wajen yaƙar ’yan adawa.

Ya kuma yi alkawarin cewa mutanen da suka yi amfani da hukumomin gwamnati wajen cin zarafin abokan hamayyar siyasa za su fuskanci alhakin ayyukansu.

“Bayan zaɓen 2027, Sowore zai zama shugaban Najeriya. Babu ja da baya,” in ji shi.

Shari’ar ta samo asali ne daga wasu saƙonnin da Sowore ya wallafa a shafukansa na X da Facebook a ranar 25 ga Agusta, 2025, inda ya kira Shugaba Tinubu da kalmar “mai laifi”.

DSS ta ba shi wa’adin kwanaki bakwai da ya goge saƙonnin, amma bayan wa’adin ya cika ba tare da ya cire su ba, hukumar ta garzaya Babbar Kotun Tarayya a ranar 16 ga Satumba, 2025.

Hukumar ta nemi kotu ta fayyace ko kiran shugaban ƙasa ko wani mutum da “mai laifi” a bainar jama’a, ba tare da wata kotu ta tabbatar da laifinsa ba, zai iya zama laifin cin zarafi ta kafafen sadarwa.

Yanzu dai DSS na shirin sanar da kotu a hukumance game da bukatar dakatar da shari’ar daga ranar 14 ga Satumba, 2026, lokacin da kotuna za su koma zaman yau da kullum bayan hutun shekara-shekara.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments