‘Yan bindiga sun kashe mutum uku, sun jikkata wasu biyar tare da yin garkuwa da Sarkin Noma na Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa, a wani hari da suka kai garin Chiromawa da ke ƙaramar hukumar Garun Malam.
Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 11 na daren Asabar, inda maharan suka nufi gidan Sarkin Noma kai tsaye tare da buɗe wuta ba kakkautawa.
Shugaban ƙaramar hukumar Garun Malam, Alhaji Aminu Salisu Kadawa, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa mutane uku sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka daban-daban.
Ya ce an kai waɗanda suka jikkata asibiti domin samun magani, yayin da jami’an tsaro suka fara farautar maharan da kuma ƙoƙarin kuɓutar da Sarkin Noma.
Kadawa ya ce ya jagoranci jami’an ƙaramar hukumar zuwa asibitin da aka kai waɗanda suka jikkata, inda suka zauna har tsawon dare domin tabbatar da cewa sun samu kulawar da ta dace.
Ya kuma buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da addu’a tare da bai wa jami’an tsaro bayanan da za su taimaka wajen gano maharan da kuɓutar da Sarkin Noma.