Wani Kirista mazaunin jihar Filato, Peter Ibrahim Gyendyeng, ya gina masallacin Juma’a domin al’ummar Musulmi da ke garin Gana Ropp, a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar.
Ginin masallacin ya haifar da farin ciki tsakanin al’ummar Musulmi da ke yankin, waɗanda suka bayyana matakin a matsayin wata babbar alama ta zaman lafiya, haɗin kai da ƙauna tsakanin mabiya addinin Musulunci da Kiristanci.
Wannan ci gaba ya zo ne a lokacin da wasu sassan jihar Filato, musamman Barkin Ladi, ke fuskantar ƙalubalen tsaro da rikice-rikicen da suka shafi dangantaka tsakanin mabiya addinan biyu.
Da yake jawabi yayin buɗe masallacin, Gyendyeng, wanda tsohon ɗan Majalisar Wakilai ne mai wakiltar mazaɓar Barkin Ladi/Bassa, ya ce ya gina masallacin ne domin ya zama wata alama ta haɗin kai da zaman tare tsakanin Musulmi da Kiristoci a yankin da ma jihar baki ɗaya.
Ya ce duk wani kuɗi da mutum zai bai wa al’umma na iya ƙarewa cikin ɗan lokaci, amma gina wurin ibada da za a riƙa yin addu’o’in neman zaman lafiya da ci gaban ƙasa abu ne da zai dawwama.
Gyendyeng ya ƙara da cewa hanya mafi kyau ta taimaka wa mutane ita ce a ba su abin da suke matuƙar buƙata da kuma ƙauna.
Da yake mayar da jawabi, babban limamin masallacin, Sheikh Ladan Gana Ropp, ya bayyana farin cikin al’ummar Musulmi kan wannan abin alheri, yana mai cewa masallacin zai ba su damar gudanar da ibadarsu cikin ’yanci da kwanciyar hankali.
Limamin ya kuma yi kira ga Musulmi da Kiristoci a Barkin Ladi da sauran sassan jihar Filato da su rungumi zaman lafiya, haɗin kai, fahimtar juna da mutunta juna domin samun ci gaba mai ɗorewa.
A cewar Daily Trust, fastoci, shugabannin coci da sauran mambobin al’ummar Kirista na yankin sun halarci bikin buɗe masallacin, lamarin da ya ƙara nuna yadda matakin ya zama wata alama ta haɗin kai tsakanin al’ummomin addinan biyu.