Dakarun Operation UDO KA na rundunar sojin Najeriya sun gano tare da tono gawar marigayi Cif Ibe Anyadu, shugaban al’ummar Aggah da ke jihar Imo, daga wani kabari marar zurfi da ke cikin dajin Umudike.
Rahotanni sun ce ana zargin wasu da aka kama kan laifukan ta’addanci ne suka kashe marigayin, inda ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya amsa laifin tare da jagorantar sojoji zuwa wurin da aka binne gawar.
A cewar rundunar, nasarar ta samu ne bayan wasu hare-hare da aka kai bisa sahihan bayanan sirri, waɗanda suka kai ga cafke mutanen da ake zargi da kashe wani jami’in soja tare da ƙwace makaman gwamnati.
A ranar 2 ga Agustan 2026, ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin ya jagoranci jami’an tsaro zuwa wani kabari marar zurfi da ke cikin dajin Umudike, inda aka tono gawar marigayin a gaban iyalansa, jami’an sintiri na Ohaji/Egbema da kuma wakilan al’ummomin Aggah da Umudike.
Iyalan marigayin sun karɓi gawar domin gudanar da jana’izarsa cikin mutunci bisa al’adunsu.
Kwamandan Joint Task Force South-East Operation UDO KA, Manjo Janar Oluremi Ayobami Fadairo, ya jajanta wa iyalan mamacin tare da tabbatar musu cewa za a gurfanar da duk waɗanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa tanadin dokokin Najeriya.
Rundunar ta kuma jaddada kudurinta na ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka da tabbatar da zaman lafiya a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.