Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiYadda kididdiga da bayanai kan makarantun Kaduna zai kawo ci gaban ilimi...

Yadda kididdiga da bayanai kan makarantun Kaduna zai kawo ci gaban ilimi – AFRI-CIRD

Cibiyar Bincike da Raya Ci Gaba ta Afirka (AFRI-CIRD) ta yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa fitar da rahotannin Kididdigar Makarantu ta Shekarar 2025/2026 da kuma kididdigar yaran da ba sa zuwa makaranta, tana mai bayyana matakin a matsayin babban ci gaba wajen tsara manufofin ilimi bisa ingantattun bayanai.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, AFRI-CIRD ta jinjinawa Gwamna Uba Sani, Mataimakiyarsa Dakta Hadiza Balarabe, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna, Hukumar Ilimin Firamare ta Jihar (SUBEB) da kuma abokan hulɗar ci gaba na ƙasa da ƙasa saboda samar da abin da ta bayyana a matsayin ɗaya daga cikin ingantattun tsarin tattara bayanan ilimi a Najeriya.

Kungiyar ta ce an tattara bayanan ne ta hanyar ziyartar gidaje sama da 360,000 a dukkan ƙananan hukumomi 23 na jihar, inda aka yi amfani da tsarin Education Management Information Systems (EMIS) da kuma Geographic Information Systems (GIS) domin samar da sahihan bayanai.

Rahoton ya nuna cewa akwai yara 187,719 da ba sa zuwa makaranta a Kaduna, adadin da ya yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da hasashen da aka yi a baya na sama da yara 500,000.

AFRI-CIRD ta danganta wannan raguwa da ci gaba da gwamnatin jihar ke yi wajen saka jari a fannin ilimi, ciki har da ilimin bai ɗaya kyauta, shirye-shiryen ciyar da ɗalibai abinci a makaranta da kuma ware kashi 25 cikin 100 na kasafin kuɗin shekarar 2026 ga ilimi.

Rahoton ya kuma nuna cewa yara masu shekaru tsakanin shida zuwa 11 sun kai kashi 64.6 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta. Haka kuma, maza sun kai kashi 56.7 cikin 100, yayin da mata suka kai kashi 43.3 cikin 100.

Rahoton ya bayyana cewa yara masu nakasa sama da 4,000, waɗanda suka kai kashi 1.43 cikin 100 na jimillar yaran da ba sa zuwa makaranta, har yanzu ba su samu damar shiga tsarin ilimin boko ba.

Har ila yau, binciken ya nuna cewa sama da kashi 91 cikin 100 na iyalan da abin ya shafa sun bayyana talauci a matsayin babban dalilin da ya hana ‘ya’yansu shiga makaranta ko kuma ya sa suka daina karatu.

Rahoton ya ƙara da cewa Yankin Sanatan Kaduna ta Arewa ne ke ɗauke da kashi 51 cikin 100 na yaran da ba sa zuwa makaranta a jihar, yayin da ƙaramar hukumar Kubau ta fi kowacce yawan yaran da abin ya shafa.

Da yake magana kan rahoton, Shugaban AFRI-CIRD, Mohammed Bello, ya ce samun sahihan bayanai shi ne ginshiƙin magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.

Ya ce:

“Jihar Kaduna ta nuna ƙwazo da jajircewa ta hanyar kafa tsarin da ya dogara da sahihan bayanai domin dawo da yara cikin ajujuwa.”

Ya ƙara da cewa:

“Amma ainihin nasarar za ta ta’allaka ne kan cikakken aiwatar da tsare-tsaren, tabbatar da gaskiya da riƙon amana, da kuma haɗin gwiwa tsakanin gwamnati, al’umma da sauran masu ruwa da tsaki tare da amfani da ƙwarewar ƙasa da ƙasa.”

AFRI-CIRD ta kuma gabatar da shirin matakai uku domin tabbatar da dorewar sauye-sauyen ilimi a Kaduna.

A cewarta, matakin farko ya haɗa da kafa kwamitin yaƙi da matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta, rarraba malamai da kayan aiki bisa bayanan da aka tattara, tare da faɗaɗa shirye-shiryen tallafin kuɗi da ciyar da ɗalibai abinci.

A matsakaicin lokaci, ta ba da shawarar ƙarfafa haɗin gwiwa da masu zaman kansu, ciki har da tsarin karatun Tsangaya da Almajirai, tare da gina makarantu masu sauƙaƙa wa yara masu nakasa.

A dogon lokaci kuma, cibiyar ta ba da shawarar ƙara shirye-shiryen koyar da karatu da lissafi tun daga matakin farko, tare da ƙarfafa kwamitocin kula da makarantu (SBMCs) da ƙungiyoyin iyaye da malamai (PTAs) domin inganta ci gaba da karatu da tabbatar da tsaron makarantu.

AFRI-CIRD ta ce tsarin tattara bayanan gida-gida da Kaduna ta ƙaddamar ya samu yabo daga ƙungiyoyi irin su UNICEF da Save the Children International, tare da bayyana cewa zai iya zama abin koyi ga sauran jihohin Najeriya wajen gyaran tsarin ilimi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments