Sunday, October 18, 2026
HomeKasuwanci2030: Kamfanin Dangote na shirin fara samar da siminti tan miliyan 80

2030: Kamfanin Dangote na shirin fara samar da siminti tan miliyan 80

Kamfanin Dangote Cement ya sanar da samun ƙaruwar jarinsa daga naira tiriliyan 2.1 zuwa naira tiriliyan 2.5, sakamakon ƙarin yawan simintin da yake samarwa da kusan kashi 10 cikin 100.

A cewar kamfanin, wannan ci gaban ya nuna bunƙasar harkokin samar da siminti da kuma ci gaba da saka hannun jari domin biyan buƙatun kasuwa a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.

Kamfanin ya kuma bayyana shirinsa na ƙara ƙarfin samar da siminti daga tan miliyan 55 zuwa tan miliyan 80 nan da shekarar 2030, a wani mataki na faɗaɗa ayyukansa.

Shugabannin kamfanin sun ce wannan shiri zai taimaka wajen bunƙasa masana’antu, samar da ƙarin guraben ayyukan yi da kuma ƙarfafa ci gaban tattalin arziki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments