Shugabar Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta bayyana cewa hukumar na da ma’aikata 2,000 kacal da ke kula da al’umma sama da mutane miliyan 240 a faɗin Najeriya.
Ta ce ƙarancin ma’aikata na daga cikin manyan ƙalubalen da ke hana hukumar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata, musamman wajen sa ido kan ingancin abinci, magunguna da sauran kayayyakin da ake amfani da su a ƙasar.
A cewarta, hukumar na buƙatar a ƙara mata ma’aikata 5,000 domin ƙarfafa ayyukan sa ido, yaƙi da jabun magunguna da tabbatar da kare lafiyar al’umma.
Shugabar ta jaddada cewa ƙarin ma’aikata zai taimaka wajen inganta aikin NAFDAC da kuma ba ta damar gudanar da aikinta cikin inganci a dukkan sassan ƙasar.