Saturday, October 17, 2026
HomeIlimiHaɗa ilimin addini da na boko ne zai taimaka wajen inganta rayuwar...

Haɗa ilimin addini da na boko ne zai taimaka wajen inganta rayuwar Almajirai – Oluremi Tinubu

Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira da a ƙara ƙarfafa shirye-shiryen da za su bai wa yara Almajirai da waɗanda ba sa zuwa makaranta damar samun ilimin zamani tare da ci gaba da karatun addini.

Ta bayyana hakan ne a Abuja yayin da ta karɓi sabon Jakadan Saudiyya a Najeriya, Ambasada Yousef bin Mohammed Albalawi, da shugaban ma’aikatan ofishin jakadancin, Mohammed Bukar.

Oluremi Tinubu ta ce haɗa ilimin boko da na Larabci zai taimaka wajen ba yara ingantaccen ilimi, ƙwarewa da damar gina makomarsu ba tare da rasa ilimin addininsu ba.

Ta jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Saudiyya wajen tallafawa shirye-shiryen ilimi da ci gaban matasa, musamman yara masu buƙatar kulawa.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments