Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiAn gano ma’aikatan bogi a rundunar ’yan sanda da wasu ma’aikatun gwamnati

An gano ma’aikatan bogi a rundunar ’yan sanda da wasu ma’aikatun gwamnati

Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta bayyana cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da wasu ma’aikatun gwamnati biyar na daga cikin hukumomin da aka gano suna da mafi yawan ma’aikatan bogi.

Hukumar Yaƙi da Rashawa ta Najeriya (ICPC) ta bayyana cewa Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da wasu ma’aikatun gwamnati biyar na daga cikin hukumomin da aka gano suna da mafi yawan ma’aikatan bogi.

Shugaban ICPC, Musa Adamu Aliyu, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da sakamakon wani bincike da hukumar ta gudanar kan tsarin biyan albashin ma’aikatan gwamnati.

A cewar hukumar, an gano ma’aikata 908 da ake zargin ba sa wanzuwa a hukumomi da ma’aikatu 59, lamarin da ya janyo asarar kuɗaɗen gwamnati ta hanyar biyan albashin mutanen da ba a tabbatar da kasancewarsu a wuraren aikin ba.

ICPC ta ce ta gano cewa kusan naira miliyan 942 ne aka biya a matsayin albashi ga waɗannan ma’aikatan da ake zargi da kasancewa na bogi.

Hukumar ta bayyana cewa binciken wani bangare ne na ƙoƙarin gano hanyoyin da ake karkatar da kuɗaɗen gwamnati tare da tabbatar da cewa albashin gwamnati na zuwa ga ma’aikatan da suke aiki da gaske.

SourceRFI
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments