Gwamnatin Tarayya ta kashe karin Naira miliyan 500 a shekarar 2025 domin fitar da bayanai da nufin mayar da martani kan zarge-zargen da ake yi a kasashen Yamma cewa ana muzgunawa kiristoci a Najeriya.
Bayanan da ke dandalin bibiyar kashe kudade na GovSpend, sun nuna cewa an fitar da kudin ne a ranar 19 ga Disamba, 2025, ta hannun Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa.
A bayanin da ke jikin biyan kudin, an ce an ware kudin ne domin “gudanar da dabarun sadarwa da hulda da kafafen yada labarai na duniya domin dakile abin da gwamnati ta kira shirya farfagandar kasashen Yamma kan zargin muzgunawa Kiristoci.”
An kashe wannan kudi ne a shekarar da Najeriya ta kuma kulla yarjejeniyar dala miliyan 9 da kamfanin DCI Group na Amurka domin inganta hulda da jami’an gwamnatin Amurka kan zarge-zargen hare-haren da ake kai wa al’ummomin Kiristoci.
Takardun da aka shigar karkashin dokar Foreign Agents Registration Act (FARA) ta Amurka sun nuna cewa kamfanin lauyoyi na Aster Legal da ke Kaduna ne ya dauki DCI Group aiki a madadin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu.
Bisa yarjejeniyar da aka sanya wa hannu a ranar 18 ga Disamba, 2025, an dorawa DCI Group alhakin bayyana matakan da gwamnatin Najeriya ke dauka wajen kare al’ummomin kiristoci tare da tabbatar da ci gaba da samun goyon bayan Amurka a yaki da Boko Haram, ISWAP da sauran kungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi.
Yarjejeniyar ta tanadi biyan kamfanin Dala 750,000 duk wata, wanda zai kai Dala miliyan 9 cikin shekara guda idan aka ci gaba da kwangilar.
Wannan mataki ya biyo bayan yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya sake ayyana Najeriya a watan Oktoban 2025 a matsayin Country of Particular Concern (CPC) bisa zarge-zargen take hakkin ‘yancin addini da muzgunawa Kiristoci.
Duk da wannan mataki, an ci gaba da samun hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, inda kasashen biyu ke aiki tare wajen musayar bayanan sirri, horas da sojoji, samar da kayan tsaro, tallafin dabarun yaki da kuma yaki da ta’addanci.
Har ila yau, gwamnatin Najeriya ta wallafa abin da ta bayyana a matsayin wasikar da Shugaba Donald Trump ya aikawa Shugaba Bola Tinubu na yabo da jaddada aniyar ci gaba da taimakon Najeriya ta fuskar tsaro.
Gwamnatin Tarayya ta dade tana jaddada cewa matsalar tsaron Najeriya ta samo asali ne daga ta’addanci, fashi da makami, rikice-rikicen kabilanci da sauran laifuffuka, ba wai wata manufar muzgunawa mabiyan wani addini ba. Ta kuma ce musulmi da kiristoci duk sun sha fama da hare-haren.