Ana ci gaba da nuna damuwa a Kamaru kan dogon lokacin da shugaban ƙasar, Paul Biya, ya shafe ba tare da bayyana a bainar jama’a ba. Shugaban mai shekaru 93 ya bar ƙasar sama da kwanaki 40 da suka gabata, lamarin da ya janyo tambayoyi kan inda yake da kuma halin lafiyarsa.
Duk da rashin bayyanar tasa, an ce Biya ya ci gaba da ɗaukar wasu matakai na gwamnati, ciki har da amincewa da yarjejeniyoyin karɓar bashi da kuma naɗa wasu jami’ai a hukumar kula da harkokin man fetur da iskar gas.
Na kusa da shugaban sun ce ya tafi Turai ne domin ɗan gajeren hutu, yayin da gwamnatin Kamaru ta musanta rahotannin da ke cewa an kwantar da shi a asibiti. Gwamnati ta ce shugaban na ci gaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata daga inda yake.
Rashin ganin Biya ya janyo martani daga jam’iyyun adawa, inda wasu ke neman a duba ko har yanzu yana iya gudanar da ayyukansa. Sai dai jam’iyyar CPDM mai mulki ta yi watsi da wannan kira, tana mai cewa shugaban na nan daram a kan muƙaminsa.
A cewar gwamnatin Kamaru, babu wata doka da ta kayyade tsawon lokacin da shugaban ƙasa zai iya kasancewa a wajen ƙasar. Paul Biya, wanda ke mulkin Kamaru tun shekarar 1982, ya shahara da yawan yin dogayen tafiye-tafiye zuwa ƙasashen Turai.